Zababbun Kalaman Soyayya Hausa Love Message For Her

Zababbun Kalaman Soyayya Hausa Love Message For Her
Two people in Social Media Concept.

Zababbun Kalaman Soyayya Hausa Love Message For Her

ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA MASU SAKA SHAUKI DA ƘARA ƘARFIN SOYAYYA

Yabo da Jinjina Zai tabbata gareki ɗiyar kirki da aminchi, duk wata fata na Alkhairi Dole nai miki shi, kin zaburar da Zuciya Ta daga dogon suma na rashin irin ki a rayuwata, Zuciyata Ta Aminta Da Kalaman Ki Domin suna saka ni farin ciki, HubbyNa kece Abu mafi Ɗanɗanon Zaƙi mai canja tinani acikin rayuwata, tankaden DA nayi da kuma Reraya, Naga Ribar Shi Akan ki, HabibiNa Ina ƙaunar ki da Zuciyata da kuma Raina, Zan Cigaba da ƙaunar ki Har Zuwa Ranar Dana Daina Numfashi, Sahibata Ina Son Ki, Soyayyar ki ta rufe min idanu Bana Son Naji ko a Mafarki Labarin Soyayyar wata ɗiya Mace Sai naki HubbyNa, Samun ki Sa’a ce garen Babba Matata, Daga ƙarshe ina Fatan Sahibar Ruhina Tana cikin ƙoshin Lafiya. Sannan Ina Fatan kina Cikin Farin Ciki. Ina ƙaunar Ki.

Hausa Love Message

🖤❤💙💜💚🧡💛

Assalamu alaiki farin cikin zuciyata kuma sanyin idanuwa na, haƙiƙa kece mace ta farko wacce na yi gamo da ita karon farko, banta6a zato ko tsammanin  za’ayi wata ƴa mace wacce zata sace min dukkanin ruhi a mafi ƙanƙantar lokaci ba sai ke, amma sai gashi ba tsammani nayi kicibus da kyakkyawar fuskar da na kasa ɗauke wa kallo, Haƙiƙa kyauwun ki yakai ayi misali dashi, kinsha gaban duk mai tinani, zuciyar ki Kyakkyawa ce, tafiyar ki mai tsari ne, Rayuwar ki abar kallo da koyi ce, lallai nayo matukar Sa’ar samun mace kamar ki a cikin rayuwata Muradina, Annuri na, Kuma Shalelen Zuciyata.

🖤❤💙💜💚🧡💛

Tambarin sarautar girma da ɗaukaka nake dokowa zuwa ga sarauniyata mai mulkin birnin zuciyata haƙaƙi kece gimbiyata wacce na damƙa farin ciki na da walwala ta a karkashin inuwar kulawarki.

🖤❤💙💜💚🧡💛

Zanso ace nafi kowa matsayi a zuciyarki domin ina da yaƙinin nafi kowa ƙaunar ki shiyasa nace a kaf faɗin duniyar masoya babu tamkarki a fagen iya sarrafa zuciya da daddaɗan kalaman soyayya tabbas nayi dace da na kasance sarkin mulkin zuciyarki.

Zababbun Kalaman Soyayya Hausa Love Message For Her

Zababbun Kalaman Soyayya Hausa Love Message For Her

🖤❤💙💜💚🧡💛

Ance so aljannar duniya ban fahimci hakaba sai da na kurbi zakin ɗanɗanon zumar soyayyarki sai kawai naji nayi suman zaune uhmmm ban ankara ba sai na tsinci kaina a sararin samaniya muna shawagi cikin duniyar masoya ina baki furennin lovayya.

🖤❤💙💜💚🧡💛

bazanyi nadama ko dana sanin zaben ki da nayi a matsayin masoyiyata ba, saboda kece zuciyata ta zaba kece wacce raina ya aminta da ita, hakika burin zuciyata a gareki shine ki zama uwar ƴaƴana mukasance a tare har fitar nunmafashin mu.

🖤❤💙💜💚🧡💛

Za6in Raina kike tilo, Bani kamar ki a zuciyata, tsananin ƙaunar da nake miki zuciyata ce kawai take iya ɗauka bakina kamantawa kawai yake, kina sani farin ciki, shigowarki cikin rayuwata Ya saitamin abubuwa da dama, Dani dake rabuwar mu sai Allah ba dai ɗan adam ba, babu wata ɗiya mace mai Zaƙin baki ko daɗin murya ko kyawun jiki kona fuska, iya tafiya ko kwarji da zata ɗaukemin hankali akan ki, Ke ɗin dai kece, kece Badaɗayata na faɗa Dake zanyi rayuwa bana son kowa sai ke. Idan muna da rai Zaki zamo matata, niko zan zamo miki miji, zamuyi rayuwa mai daɗi, zan debe miki kewa zan saka ki farin ciki iya iyawata, Zan Baki Duk Abunda Kike so.

🖤❤💙💜💚🧡💛

HubbyNa Zan kasance dake ne a zuciyata Ba tare da wata fargaba ba, zan killace Soyayyar ki araina. Duk Ranar Da Nace Miki Bana sonki To Bani bane Sai dai wanina, Inason muyi zama na amana, mu baiwa junan mu yarda, kada musa raini a lamarin mu domin cigaban farin cikin mu muyi so dan Allah Na Gaskiya.

Check Also: Kalaman Soyayya Na Hausa Love Message For Her, Sakon Love, Soyayya Quotes

🖤❤💙💜💚🧡💛

Kyakkyawar zuciya tana rayuwa ne ƙarƙashin inuwar aminci,da amincewa, zuciyar da  aka cudanyata da tsarkakekkiyar soyayya tana Samar da ingantacciyar lafiya agangar jikin mamallakinta, Haƙiƙa zuciya kalmace tamusanman don  soyayya, soyayya kalmace ta musanmace don kulawa, ita kuma kulawa kalmace ta musanman domin ke, ke ta musanman ce agare ni… Ina yiwa Allah godiya daya bani nagarcecciyar mace irinki my unforgettable.

🖤❤💙💜💚🧡💛

Kada ku manta ku yi subscribe din wannan page din domin sanar daku da zarar mun dora sabon posting.

Muna Godiya da irin Gudummawan da kuke bamu. Muna tare daku iya wuya.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*